Kalaman jami'ar kasar ta Kenya na zuwa ne kwanaki uku bayan harin da a kai kan wani otel dake da rukunin shaguna a Nairobin kasar Kenya.
Monica Juma ta kuma bayyana kudurin kasar ta Kenya na yaki da duk wani nau'i na ta'addanci, tana mai cewa, jami'an tsaro za su bankado tare da hukunta duk wadanda ke da hannu cikin harin na Nairobi da ya yi sanadiyar rayukan mutane 21 kana wasu da dama kuma suka jikkata.(Ibrahim)