Kamfanin ya ce zai samarwa lardin Gansu kimanin kilowatt miliyan 600 na hasken wutar lantarki, yayin da wasu larduna dake arewaci da tsakiya da kuma kudu maso yammacin kasar Sin za su samu kilowatt miliyan 400.
Allah ya albarkaci yankin Tibet na kasar Sin da makamashi mai tsafta. Ya zuwa karshen shekarar 2017 da ta gabata, yankin ya tara makamashi mai tsafta da yawansa ya kai kilowatt miliyan 2.57 wanda ya kunshi wutar lantarki bisa karfin ruwa da kuma hasken rana. (Ibrahim)