A gun taron ayyukan sufuri na yankin Tibet na shekarar 2019, shugaban hukumar kula da harkokin sufuri ta yankin Yong Ji ya bayyana cewa, yawan jarin da aka zuba kan sufurin hanyoyin motoci a shekarar 2018 ya kai Yuan biliyan 65.2, wanda ya karu da kashi 14.6 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar 2017, wanda ya kai kashi 31.4 cikin dari bisa adadin jarin da aka zuba a yankin. Yankin ya yi amfani da jarin da gwamnatin kasar ta bayar da yawansa ya kai Yuan biliyan 28.17, wanda ya karu da kashi 66.4 cikin dari bisa na makamancin lokacin shekarar 2017. Tsawon sabbin hanyoyin motoci da aka gina ya kai kilomita 8044, kana tsawon hanyoyin motoci a dukkan yankin ya kai kilomita dubu 97.4. (Zainab)