in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar NPC ta Sin ta yi watsi da dokar Amurka game da Tibet
2018-12-21 10:41:52 cri

Majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ta NPC, ta yi fatali da dokar gwamnatin Amurka game da sha'anin yankin Tibet, wadda ta tanaji daukar matakan gurgunta kudurin kasar Sin, na kara bude kofar yankin na Tibet ga sauran sassan duniya.

Wata sanarwa da ofishin kwamitin harkokin waje na majalissar ta NPC ya fitar a daren jiya Alhamis, ta ce dokar ta gwamnatin Amurka ta tanaji nuna wariya ga jami'an babban yankin kasar Sin game da batun mallakar Visa, wanda hakan ya sabawa dokoki na kasa da kasa, baya ga kutsa kai cikin harkokin gida na kasar Sin da dokar ta yi. Har ila yau dokar za ta aike da wani irin sako mai hadari ga masu rajin ballewar yankin na Tibet.

Sanarwar ta jaddada matsayin kasar Sin na kare ikon mallakar yankunan ta, tana mai cewa batun Tibet, da sauran larduna 4 dake kewayen sa, batu ne na cikin gidan kasar Sin, wanda bai dace wata kasa ta tsoma baki a cikin sa ba, kuma dukkanin yankunan ana bude kofar su ga sassan duniya baki daya.

Tun daga shekarar 2015, adadin masu ziyartar Tibet da yankunan dake makwaftaka da shi na ta karuwa, inda Amurkawa kadai da suka ziyarci yankin suka doshi mutum 40,000, ciki hadda tawagogin majalissar dokokin kasar Amurkan, wadanda majalissar NPC ke karbar bakunci.

Majalissar NPC dai ta ce dokar ta Amurka ta yi watsi da hakikanin gaskiyar al'amari, tana kuma cike da nuna kyama da rashin adalci, matakin da Sin ba za ta taba amincewa da shi ba.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China