in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ta bukaci a kara tallafawa matasan Afrika a lokacin da ake tsakan da samun yawan jama'a
2017-10-27 09:58:49 cri

Asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ya bukaci a kara raya harkokin matasa tare da na lafiya da ilimi da kare mata da karfafa musu a nahiyar Afrika.

Wani rahoton asusun ya ce, idan nahiyar ta samu sauyi wajen rage mace-mace da hayyafa tare da samun ci gaba, matasa 'yan kasa da shekaru 18 za su kai miliyan 750 zuwa shekarar 2030.

Rahoton ya ce akwai bukatar kara kaimi wajen inganta harkokin lafiya da ilimi da kare hakkokin mata ko kuma nahiyar ta fuskanci rashin kyakkyawar makoma.

A cewar Daraktar asusun a yankunan yammaci da tsakiyar Afrika Marie-Pierre Poirier, idan nahiyar ta zage damtse wajen inganta rayuwar yara da matasa a yanzu, ta kuma sauya tsarin ilimi tare da karfafawa mata da 'yan mata ta yadda za su shiga a dama da su cikin al'umma da wuraren aiki da siyasa, nahiyar za ta gaggauta cimma moriya mai yawa daga sauyawar yanayin al'umma, inda jama'a za su samu ayyukan yi, ta yadda za su bada gudummuwa wajen ciyar da nahiyar gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China