in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana ta yi bikin cika shekara 62 da samun 'yancin kai
2019-03-07 09:37:22 cri

A jiya Laraba kasar Ghana ta gudanar da bikin murnar cika shekaru 62 da samun 'yancin kanta a babban filin taro na Aliu Mahama dake Tamale, yankin dake arewacin babban birnin kasar, mai tazarar kilomita 618 dake shiyyar arewacin Accra, babban birnin kasar.

Daruruwan jama'a da suka fito daga fannonin rayuwa daban daban na kasar ne suka hallara don gudanar da faretin girmamawa ga kasar. Wannan shi ne karon farko da aka gudanar da bikin murnar samun 'yancin kasar a wajen birnin Accra.

Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya bukaci 'yan kasar da su sanya kishin kasa da kaunar ci-gaban kasar a cikin zukatansu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China