in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin zata ba da taimako don fadada jami'ar nazarin kiwon lafiya ta Ghana
2019-01-12 16:11:23 cri

A jiya Juma'a, kasar Sin ta yi alkawarin taimakawa kasar Ghana wajen fadada jami'ar nazarin kiwon lafiya da fasaha ta yankin Ho, mai tazarar kilomita 180 a arewa maso gabashin babban birnin kasar, Accra.

A wani kwarya kwaryar biki da aka shirya, jakadan kasar Sin a Ghana, Wang Shiting, da ministan kudin kasar Ghana Ken Ofori-Atta, sun sanya hannu kan takardar tallafin a madadin kasashen biyu.

Wang ya ce, sanya hannu kan yarjejeniyar alamu ne dake nuna cewa gwamnatin kasar Sin za ta taimaka wajen gudanar da zagaye na biyu na aikin fadada jami'ar nazarin lafiya da kimiyya ta kasar Ghanan

."Wannan kyauta ce daga gwamnatin kasar Sin da al'ummar Sinawa zuwa ga gwamnatin Ghana da jama'ar kasar Ghanan. Kana wani mihimmin mataki ne na kara karfafa dankon zumunta dake tsakanin kasashen biyu," inji jakadan.

Kashin farko na aikin, ya kunshi fili mai fadin kadada 10,386, shi ma gwamnatin kasar Sin ne ta samar da kudaden gudanar da aikin. Aikin wanda aka mika shi ga gwamnatin kasar Ghana a watan Satumbar shekarar 2015, ya kunshi wasu muhimman kayayyakin aikin gwaje gwajen kimiyyar kiwon lafiya da kimiyyar tsirrai, da manyan dakunan daukar darasi na dalibai, da dakunan karatu, da gine ginen dakunan kwanan dalibai, da kuma rukunin gidajen kwanan manyan ma'aikata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China