in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
CEIEC zai taimakawa kasar Ghana ta bunkasa albarkatunta na gandun daji
2019-01-23 11:17:23 cri
Kamfanin kayayyakin shige da fice na laturori na kasar Sin (CEIEC) da hukumar kula da gandun daji ta kasar Ghana, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna a jiya Talata, da nufin karfafa alakarsu a fannin bunkasa albarkatun gadun daji.

A karkashin wannan yarjejeniya, kasashen Sin da Ghana za su kaddamar da aikin hadin gwiwa a fannin gandun daji, lamarin da zai baiwa kasashen biyu damar kafa yankin raya gandun daji, da taimakawa kasar Ghana amfana da albarkatunta na gandun daji.

Shugaban hukumar CEIEC Liu Zhirong wanda ya sanya a madadin kamfaninsa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, alakar za ta taimakawa kasar Ghana sarrafa albarkatunta na gandun daji ta yadda zai amfani al'ummarta a fannoni daban-daban.

An dade ana sukar yadda kasar Ghana ke kula da albarkatunta na gandun daji, saboda rashin mai da hankali kan yadda za a dade ana cin gajiyarsa, sakamakon matsaloli da suka hada da rashin ci gaba mai dorewa, da dada ake sare bishiyoyi ba bisa tsari ba, da karancin fasahohi da kayan aiki na samar da katako da ma yadda ake sarrafa shi. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China