in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Ghana ta amince da dokar amfani da jirage marasa matuka a fannin lafiya
2018-12-12 10:19:35 cri
Rahotanni daga kasar Ghana na cewa, majalisar dokokin kasar ta amince da dokar da za ta ba da damar amfani da jirage marasa matuka wajen jigilar kayayyakin kiwon lafiya.

Amincewar da majalisar dokokin kasar ta yi kan wannan doka, na nufin cewa, ma'aikatar lafiyar kasar da abokiyar huldarta Zipline International Inc. za su bullo da managartan matakan da za su tabbatar da yadda za a rika jigilar muhimman kayayyakin kiwon lafiya zuwa asibitoci da sauran cibiyoyin lafiya a kan lokaci ba tare da wata matsala ba.

A cewar jami'ai da zarar komai ya kammala a shekarar da ke tafe, kasar Ghana za ta kasance kasa ta farko a yammacin Afirka, dake amfani da tsari na jigilar kayayyakin lafiya da jirage marasa matuka. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China