Jian Weihong, mataimakiyar shugaban kamfanin zuba jari a kasashen dake cikin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya wato China Silk Road Development Capital Management Company LTD, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, manufar kamfaninsu ita ce, taimakawa wajen inganta harkokin kiwon lafiya.
Jian Weihong, ta sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da wakilan kasashen da za su ci gajiya aikin a jiya Laraba, yayin bikin bude taron yini 3 kan kiwon lafiya a yankin yammacin Afrika, wanda ke gudana a birnin Accran Ghana. (Fa'iza Mustapha)