Kakakin ofishin kare hakkin bil adama Ravina Shamdasani ta fada a taron manema labarai cewa, an jiyo Bachelet tana cewa, "tare da nuna takaici mun riga mun rufe ofishinmu a Burundi bayan shafe shekaru 23 yana gudanar da aiki a kasar" tun daga ranar 28 ga watan Fabrairu.
Shekaru biyu ke nan tun bayan da aka dakatar da hadin gwiwa, a ranar 5 ga watan Disambar 2018, gwamnatin kasar Burundi ta bukaci a rufe ofishin kare hakkin dan adam na MDD a kasar.
Gwamnatin kasar Burundi ta ce kasar ta samu ci gaba mai yawa wajen daukar matakan bada kariya ga hakkin adam, don haka ci gaba da zaman ofishin ba shi da wata hujja. (Ahmad Fagam)