Shugaban ya yi wannan kira ne a jiya Litinin, yayin bikin cika shekaru 56 da samun 'yancin kan kasar, wanda ya gudana a birnin Bujumbura, fadar mulkin kasar.
Manyan jagororin kasar ta Burundi ciki hadda shugaban ta Pierre Nkurunziza, da shugabannin majalissun dokokin kasar biyu, da kusoshin gwamnati, da jami'an diflomasiyya dake kasar da dama sun halarci bikin.
Kaza lika al'ummar kasar, da sassan rundunonin tsaron kasar, sun gudanar da fareti domin taya murnar wannan biki. Baya ga hakan an kuma yi wasu nune-nune domin nishadantar da al'umma.
A daya hannun kuma, shugaban kasar da manyan jami'ai, sun gudanar da karin wasu bukukuwan a wurare 2, da suka hada da ziyartar harabar ginin tunanwa da yarima Louis Rwagasore dake tsaunin Vugizo, da kuma aza furanni a filin taro na tunawa da samun 'yancin kan kasar ta Burundi. (Saminu Hassan)