in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da zanga-zanga a Burundi kan furucin wakilin MDD dake kasar
2018-06-03 15:38:52 cri
Gwamnatin kasar Burundi, ta shirya wata zanga-zanga a fadin kasar jiya Asabar, game da furucin da wakilin musammam na MDD a Burundi Michel Kafando ya yi, wanda ke cewa, kuri'ar raba gardama kan gyaran kundin tsarin mulkin kasar da aka yi, zai kara ta'azzara halin da ake ciki a yanzu.

Ministan harkokin cikin gidan kasar Pascal Barandagiye, wanda shi ma ya shiga zangar-zangar, ya shaidawa jama'a a garin Ngozi na Lardin Ngozi dake arewacin Burundi cewa, zanga-zangar da suka gudana a manyan garuruwan Burundi a dukkan larduna 18, na kuma da nufin nuna adawa da Gwamnatocin Faransa da Belgium na raba kan al'ummar kasar.

A farkon makon da ya wuce ne, ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar da wata sanarwar da ta bayyana cewa, kundin tsarin mulkin da aka gyara bai bada kariya ga karamin kabilar Tutsi ba.

A cewar Minstan, ya kamata Faransa da sauran masu mulkin mallaka kamar Belgium, su daina tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar.

Jam'iyyar CNDD-FDD mai mulkin Burundi, ta ce kundn tsarin da aka yi wa gyaran fuska, na girmama yarjejeniyar Arusha ta shekarar 2000, wadda ta tanadi yadda za a raba mukamai da da hukumomin gwamnati tsakanin kabilu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China