in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika aikin samar da sadarwar tauraron dan Adam na talabijin ga kauyukan kasar Burundi 300
2019-03-02 16:04:27 cri

Gwamnatin kasar Sin, ta mika aikin samar da sadarwar tauraron dan Adam ta talabijin ga gwamnatin kasar Burundi, wanda kauyukan kasar dake yammacin Afrika za su ci gajiya.

Aikin na daga cikin sakamakon taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika wato FOCAC na 2015 da aka yi a Afrika ta Kudu, inda gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin samar da sadarwar tauraron dan Adam ta talabijin ga kauyuka 10,000 na kasashen Afrika 25.

Da yake jawabi kafin sanya hannu kan daftarin mika aikin ga ministan sadarwar kasar Fedric Nahimana a birnin Bujumbura, Jakadan kasar Sin Li Changlin, ya ce aikin zai yi kyakkyawan tasiri ga yankuna daban-daban na Burundi, sannan zai kara inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da kasar.

Ya kara da cewa, aikin na da dimbin fa'ida ga al'umma, domin zai taimakawa mutanen dake kauyuka samun bayanan abubuwan dake faruwa a ciki da wajen kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China