Yayin zantawarsa da manema labarai a babban birnin Bujumbura ya ce, kasar na fatan kara zurfafa hadin kai da Sin a dukkanin fannoni. Sannan kasar Burundi na sa ran kara hadin kai da Sin a fannoni daban-daban, kuma tana goyon bayan taron da Sin za ta gudanar a wannan karo. A cewarsa, yayin taron kolin AU, kasashen Afrika sun bayyana kasar Sin a matsayin tsohuwar aminiya ta kwarai, wadda ta ba su taimako sosai. (Amina Xu)