in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika gidan gwamnatin da ta taimaka wajen ginawa kasar Burundi
2019-02-15 10:09:32 cri
Jakadan kasar Sin a Burundi, Li Changlin da ministan harkokin wajen Burundi Ezechil Nibigira, sun sanya hannu kan daftarin mika sabon gidan gwamnatin kasar da Sin ta taimaka wajen ginawa.

Yayin bikin sanya hannun da ya gudana sabon gidan gwamnatin dake lardin Mutimbuzi dake arewacin babban birnin kasuwancin kasar wato Bujumbura, Jakada Li ya ce sanya hannu kan daftarin alama ce ta aminci da dangantakar dake tsakanin Sin da Burundi.

Li Changlin, ya ce ya tattara masu fassara da za su fassara jadawalin ci gaban kasar Burundi zuwa harshen Sinanci, wanda zai taimaka wajen gano muhimman bangarorin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa, dangantakar da ke tsakaninsu za ta mayar da hankali ne kan inganta rayuwar al'ummar kasar da ma yanayin aiki ga ma'aikatan gwamnati.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Burundi, ya godewa kasar Sin da ta ba kasarsa gidan gwamnatin da ba ta taba mallaka ba, tun bayan da ta samu 'yancin kai a ranar 1 ga watan Yulin 1962.

Ya ce gwamnatin Burundi, za ta ci gaba da yin bakin kokarinta wajen habaka dangantakar dake tsakaninta da Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China