Daliban uku, wadanda suka samu nasara daga cikin dalibai 11 da suka fafata a gasar, su ne za su wakilci kasar ta Zambia a gasar ICT da aka shirya ta shiyya a kasar Afrika ta kudu daga ranar 8 zuwa 9 ga watan Maris.
Nkandu Luo, ministan ma'aikatar ilmi mai zurfi na kasar, ya yabawa kamfanin sadarwar na kasar Sin saboda shirya gasar wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen bunkasa cigaban fasahar sadarwa ta zamanin a kasar ta kudancin Afrika. (Ahmad Fagam)