in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani hari a jihar Sokoton Nijeriya ya yi sanadin mutane 16
2019-02-27 09:51:43 cri
Mutane a kalla 16 aka tabbatar sun mutu, yayin wani harin da aka kai jihar Sokoto dake arewa maso yammacin Nijeriya.

Yayin wani taron manema labarai jiya, gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal, ya ce al'amarin ya auku ne a ranar Litinin da dare, a yankunan Dalijan da Rakkoni da Kalhu, wadanda ke yankin karamar hukumar Rabah na jihar.

Gwamna Tambuwal ya kuma gargadi 'yan siyasa game da furta kalamai ko yin abubuwan da za su harzuka jama'a, bayan zaben da aka kammala.

An gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin tarayya ne a ranar Asabar da ta gabata karkashin matakan tsaro masu tsauri a duk fadin kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China