Wata majiya daga rundunar 'yan sanda, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an samu gawarwakin mutanen ne a kauyukan da suka hada da Karamai da Gidan Gajere da Gidan Auta da kuma Chibiya, wadanda ke karkashin garin Maro, inda kuma 'yan sanda masu mukamin supeto guda 2 suka bata.
Majiyar ta ce an tura jami'an tsaro kauyukan da aka samu gawarwakin, tana mai cewa an samu galibin gawarwakin ne a kauyukan Karamai da Gidan Auta, sannan an kone gidaje sama da 40 a kauyukan.
Ta kara da cewa, daga cikin mutanen 27 har da wani dan sanda da maharan suka kashe a lokacin da yake bin sahunsu.
Cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa jami'an tsaro na aiki domin kwantar da kura a yankin. (Fa'iza Msutapha)