Taron kolin wanda aka fara a ranar 7 ga wannan watan, zai share fage ne wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a birnin Paris, ana tunanin lamarin zai iya daukar sabon salo sakamakon nasarar da dan takarar jamiyyar Republican Donald Trump ya samu a zaben shugabancin Amurka.
Dama dai tun a lokacin yakin neman zabensa, mista Trump, ya bayyana batun na sauyin yanayi da cewa tamkar "wasan yara ne" kuma ya lashi takobi soke duk wasu kudurori da gwamnatin Obama ta dauka, musamman game da rattaba hannun da Amurkar ta yi kan yarjejeniyar Paris.