in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masana kimiyya a Afrika sun yi kira da a inganta matakan kula da dazuka don magance sauyin yanayi
2017-05-23 10:00:35 cri

Masana kimiyya sun bayyana cewa, ba da cikakkiyar kulawa ga dimbin albarkatun dazuka a yankin kudu da hamadar Sahara, ita ce muhimmiyar hanyar tunkarar matsalar sauyin yanayi da ta addabi yankin take kuma yi mata mummunan tasiri.

Masana kimiyya da masu bincike sun shaidawa wani taro a Entebbe na Uganda cewa, idan za a iya kula da albarkatun dake dazuka yadda ya kamata, to za a iya samun ci gaba ta fuskar kare dazuka a Afrika.

Sakataren zartarwa na kungiyar kare dazuka ta Afrika dake zamanta a Nairobi, Godwin Kowero, ya ce nahiyar ba za ta cimma burinta na kare tsirrai ba har sai kasashen yankin sun inganta kula da abubuwa masu daraja kamar dazuka da muhallan rayuwar tsirrai da halittu.

Gomman masana kimiyya na kasashen Afrika da masu ruwa da tsaki ne ke halartar taron na yinin 5, don tattauna sabbin dabarun sake farfado da kare dazuka a lokacin da ake tsaka da fuskantar sabbin barazana.

Kowero ya ce, har yanzu, kasashen Afrika ba su amfani da albarkatun dake dazuka don magance sauyin yanayi da talauci, yana mai alakanta matsalar da rashin wayewar kai da kuma rashin matakan da suka dace.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China