in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin AfDB zai samar da kudaden tallafi ga kasashen Afrika 5 don yaki da sauyin yanayi
2017-05-04 08:48:14 cri

Bankin raya ci gaban kasashen Afrika (AfDB), zai samar da kudi kimanin dalar Amurka biliyan 1.1 ga Najeriya da wasu kasashen Afrika 4 domin shawo kan matsalolin sauyin yanayi.

Akinwumi Adesina, shi ne shugaban bankin na AfDB, ya fadi hakan ne a sakon fatan alheri da ya gabatar a lokacin taron kolin na shirin samar da abinci a Najeriya wato Feed Nigeria Summit da aka gudanar a Legas, birnin kasuwancin kasar, ya ce, bankin zai nemi amincewar kwamitin zartaswarsa domin ya ba shi damar ba da tallafin kudin da ya kai dala biliyan 1.1 ga kasashen Najeriya, Sudan ta Kudu, Kenya, Habasha da kuma Somalia domin su gudanar da ayyukan matsakaici da dogon zango na yaki da sauyin yanayi.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China