in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sinohydro ya rattaba hannu kan kwangilar ginin titi da gwamnatin Habasha
2019-01-17 10:10:21 cri
Hukumar raya tituna ta kasar Habasha, ta sanya hannu kan wata kwangila ta ginin babban titin mota da kamfanin gine-gine na kasar Sin wato Sinohydro Corporation, aikin da zai lashe kudi har dalar Amurka miliyan 33.

Cikin wata sanarwar da aka fitar game da yarjejeniyar aikin, an ce kamfanin Sinohydro zai daga matsayin babbar hanyar Gedo zuwa Menabegna, inda za a mayar da ita mai kwarin gaske. An ce tsawon hanyar ya kai kilomita 80.5. Bankin Raya Afirka na AfDB, da wasu cibiyoyin kudi na gabas ta tsakiya ne za su samar da kudin gudanar da aikin.

Gwamnatin kasar Habasha na aiwatar da manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa ciki hadda titunan mota a sassan kasar, a wani mataki na fadada hanyoyi da ake fatan za su daga daga kilomita 100,000 a shekarar 2015 zuwa kilomita 200,000 nan da shekarar 2020.

A baya bayan nan hukumar ERA ta shelanta cewa, tsawon hanyoyin mota a kasar ya karu, daga kasa da kilomita 19,000, zuwa kilomita 113,000 cikin shekaru 27 da suka gabata. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China