in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira ga dukkan bangarori a Najeriya dasu kai zuciya nesa don kaucewa rikicin bayan zabe
2019-02-26 09:32:49 cri
Tawagar jami'an sa ido a zaben Najeriya ta kungiyar tarayyar Afrika (AU) wato (AUEOM), a jiya Litinin ta bukaci dukkan jamiyyun siyasar kasar da 'yan takara dasu martaba gudanar zabe cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali kana su warware bambance-bambance dake tsakanin su.

Kungiyar ta Afrika mai mambobin kasashe 55, a yayin da aka fara bayyana sakamakon farko na zaben shugaban kasar a ranar Litinin, ta bukaci dukkan jam'iyyun siyasar Najeriyar dasu gargadi magoya bayansu su kwantar da hankula kuma su zauna lafiya da juna, kana su kaucewa daukar duk wani mataki da zai iya haifar da tunzuri bayan an bayyana sakamakon zabukan kasar.

A cikin sanarwar da aka bayar, an ce "Koda an samu wata takaddama game da sakamakon zaben, kamata yayi jam'iyyun siyasar da 'yan takara su dauki matakan kalubalantar sakamakon zaben a gaban shara'a."

Tawagar ta AU ta kuma bukaci al'ummar Najeriya da dukkan masu ruwa da tsaki dasu guji yin amfani da kafafan sada zumunta na zamani wajen yada bayanan karya game da sakamakon zaben.

A cewar AU, zabukan na ranar 23 ga watan Fabrairu, su ne zabuka na 6 da aka gudanar a kasar a jere tun bayan da kasar ta koma tsarin mulkin demokaradiyya a shekarar 1999, hakan yana nuna cewa kasar ta yammacin Afrika ta fara komawa turbar mulkin demokaradiyya. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China