in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Burundi ya buga wasan kwallon kafa tare da alummar Sinawa mazauna kasarsa
2018-04-01 13:12:02 cri
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza a ranar Asabar ya taka leda a wasan kwallon kafa da ya buga tare da al'ummar Sinawa mazauna Burundi a lardin Ngozi dake arewacin Burundi.

Tawagar 'yan wasan Nkurunziza, ta hada da shugaban kasar da tsoffin fitattun 'yan wasan kwallon kafan kasar da suka yi ritaya daga wasa, sun lashe gasar wasan kwallon kafan da aka gudanar, inda al'ummar Sinawa da 'yan kasar Burundi suka kalli wasan cikin hadin gwiwa.

Jakadan kasar Sin a Burundi Li Changlin, da sauran jami'an diplomasiyyar kasar Sin, da ma'aikatan kamfanonin kasar Sin da Sinawa mazauna kasar Burundi sun halarci wasan na tsawon mintoci 90.

Nkurunziza ya buga wasan har zuwa karshe duk kuwa da kasancewar ana ruwan sama a lokacin wasan.

Bayan kammala wasan, jakadan kasar Sin ya baiwa Nkurunziza rigar 'yan wasa mai dauke da sunan shugaban kasar. Kana ya mika wasu kayayyakin wasanni ga shugaba Nkurunziza. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China