in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira ga kasashen duniya masu karfi su daina tsoma baki cikin harkokin kasar Libya da yaki ya daidaita
2019-02-12 11:51:16 cri
Kwamishinan kwamitin sulhu na Tarayyar Afrika Smail Chergui, ya yi kira ga kasashen duniya masu karfi, da su daina tsoma baki cikin harkokin kasar Libya da yaki ya daidaita.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudana a gefen taron AU na 32, Smail Chergui ya ce al'ummar Libya sun sha wahala sosai sakamakon yakin basasa da tsoma baki da kasashen duniya masu karfi suka yi cikin harkokin cikin gidan kasar, yana mai bukatar a dakatar da duk wata tsoma baki da ba a bukata nan take.

Sai dai kuma, bai bayyana sunayen kasashen da yake zargi da tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Libyan ba, wanda ke illa ga al'ummar kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China