Hukumar ta ce duk da raguwar bautar da yara a duniya, abun takaici ne yadda har yanzu galibin kasashen da ake aiwatar da mummunar dabi'ar suka kasance a nahiyar Afrika.
Wata sanarwa da hukumar ta AU ta fitar a jiya, ta ce har kullum, nahiyar Afrika na cikin wadanda ke fama da matsaloli da rikice-rikice, wadanda ke kara hadarin bautar da yara.
A cewar wani rahoto na 2016, da ya yi kiyasin yaran da ake bautarwa a duniya, 1 bisa 5 na yaran nahiyar Afrika sun yi aikin bauta. Haka zalika, ya yi kiyasin yara miliyan 72.1 na cikin aikin bauta, kuma miliyan 31.5 na ayyuka masu hadari, wadanda suka fi yawa a bangaren aikin noma da hakar ma'adinai. (Fa'iza Mustapha)