in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin zai ziyarci Tajikistan, da Netherlands, da Belgium da nufin bunkasa hadin gwiwa
2018-10-10 09:56:28 cri
Firaministan Sin Li Keqiang, zai ziyarci kasashen Tajikistan, da Netherlands, da Belgium, tare da halartar wasu tarukan inganta hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin ta fitar, ta nuna cewa tsakanin ranekun 11 zuwa 19 ga watan nan ne firaminstan zai gudanar da wannan ziyara. Da fari dai firaminista Li Keqiang, zai halarci taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO karo na 17, wanda zai gudana a birnin Dushanbe na Tajikistan, kana zai gana da shugabannin kasar ta Tajikistan.

Daga nan zai kai ziyara kasar Netherlands, sannan zai halarci taron ASEM na hadin gwiwar Sin da kasashen Turai karo 12, wanda zai gudana a birnin Brussels, kafin ya gudanar da ziyarar aiki a kasar ta Belgium.

Da yaka karin haske game da wannan ziyara, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Hanhui, ya ce ziyarar Mr. Li na da matukar muhimmanci, wajen inganta hadin kai tsakanin kasashe mambobin kungiyar ta SCO, da ma tsakanin Sin da kawayenta na Turai. Kana za ta inganta dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen da Tajikistan, da Netherlands da kuma Belgium.

Ana sa ran yayin taron shugabannin SCO, Mr. Li zai yi karin haske game da tunanin shugaban kasar Sin Xi Jinping, game da salon mulkin gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin a sabon zamanin da ake ciki, tare da fayyace irin nasarori da Sin ta samu, sakamakon gyare gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje da take aiwatarwa.

Kaza lika Li Keqiang, zai yi tattaunawa mai zurfi da shugabannin Asiya da na Turai, kana ya gabatar da jawabai, tare da yin kira ga dukkanin sassa, da su kara kwazo wajen shawo kan kalubalen dake addabar su baki daya.

Har wa yau firaministan na Sin, zai gabatar da shawarar Sin ta kyautata hadin gwiwa tsakanin Asiya da Turai, ya kuma gabatar da mahangar kasar sa game da batutuwan kasa da kasa, da na shiyya shiyya, wadanda suka fi jawo hankulan daukkanin sassa. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China