Madan Hua ta bayyana hakan ne yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa. Rahotanni na cewa, a kwanakin baya ne dai Senata Rubio ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, ya damu matuka kan yadda mahukuntan kasar ta Sin ke murkushe mabiya addinin Kirista a kasar. Yana mai cewa, ana kuma tilastawa musulmai a yankin Xinjiang aikin kwadago da matsa musu lamba. Ya ce matakan kasar Sin na kawar da addini ya keta 'yancin dan-Adam
Sai dai madam Hua ta ce sanarwar da Rubio ya fitar shirme ne kawai, kuma wannan wata alama ce dake kara nuna rashin hankali wasu Amurkawa. (Ibrahim)