in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Rasha za su kyautata mu'amalar tattalin arziki
2018-11-08 13:43:41 cri
Kasashen Sin da Rasha sun amince a jiya Laraba za su kara kyautata tsarin siyasa da amincewa juna wajen raya mu'amalar ciniki da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Wannan yarjejeniya ta zo ne a lokacin da firaiministan kasar Sin Li Keqiang da takwaransa na Rasha Dmitry Medvedev, suka jagoranci taron tattaunawar manyan jami'an gwamnatocin kasashen Sin da Rasha karo na 23 a birnin Beijing.

Da yake nuna yabo dangane da saurin bunkasuwar mu'amalar cinikayya da tattalin arziki da aka samu tsakanin Sin da Rasha tun daga farkon wannan shekara, Li ya ce, mu'amalar cinikayya tsakanin kasashen biyu ta zarta na dalar Amurka biliyan 100 ya zuwa karshen wannan shekara, kuma akwai alamun samun kyakkyawar makoma a nan gaba.

Ya bukaci bangarorin biyu da su kara kyautata mu'amalar cinikayyarsu, da fadada mu'amalar zuba jari, da kara kyautata mu'amalar hadin gwiwa a fannin aikin gona, da kara bunkasa mu'amalar ciniki ta intanet a dukkan iyakokin kasashen, da kuma kara bunkasa mu'amalar hadin gwiwa a fannonin kirkire kirkire, musamman a fannin kimiyya da fasaha da yin nazarce nazarce.

Kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Rasha wajen cimma nasarar aiwatar da muhimman ka'idojin kungiyar ciniki ta duniya WTO domin kiyaye tsarin ciniki cikin 'yanci da na gamayyar kasa da kasa, in ji Li.

A nasa bangaren, Medvedev, ya jaddada alfanun dake tattare da kyakkyawar alakar dake tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa, kasar Rasha a shirye take ta kara zurfafa mu'amalarta da kasar Sin a dukkan fannoni, da kuma kara zurfafa mu'amalar hadin gwiwa a fanin cinikayya a tsakaninsu.

Kana ya bayyana kwarin gwiwa game da samun bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu a fannonin kirkire kirkire, ciniki ta hanyar intanet, aikin gona, makamashi, da makamashin nukiliya da kuma harkokin sufuri.

Manyan jami'an gwamnatocin kasashen biyu sun amince su kara zurafafa hadin gwiwarsu domin tabbatar da tsarin gamayyar kasa da kasa, da ciniki cikin 'yanci bisa ga dokokin kungiyar WTO. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China