in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD: 'Yan gudun hijira suna komawa gidajensu daga Kamaru zuwa Najeriya duk da matsalar tsaro
2019-03-01 09:49:32 cri

Kakakin MDD ya bayyana jiya Alhamis cewa, kimanin 'yan gudun hijira 10,000 ne suka koma gidajensu a arewa maso gabashin Najeriya, duk kuwa da tashin hankalin da ake fuskanta a yankin.

Ofishin kula da samar da jin kan al'umma na MDD (OCHA) ya ba da rahoton cewa, kimanin 'yan gudun hijira 10,000 ne suka koma gidajensu a ranar Laraba zuwa garin Rann a arewa maso gabashin Najeriya daga jamhuriyar Kamaru," in ji Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres.

"Wadannan fararen hula suna daga cikin mata da maza da kananan yara 40,000 wadanda tashin hankali ya tilasta musu tserewa daga garin Rann bayan munanan hare-hare da mahara suka yi a watan Disambar 2018," in ji Dujarric.

Kakakin MDD ya fada wa manema labarai cewa, hukumomin ba da agaji na kasa da kasa ba su iya shiga Rann domin samar da kayayyakin tallafin jin kai ba sakamakon rashin tsaro dake addabar yankin tun daga tsakiyar watan Janairu.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD wato UNHCR sun ce, hare-haren da mayakan Boko Haram suka yi wadanda suka lalace tsaron Najeriya, sun tilastawa mutane tsere zuwa Kamaru a watan Disamba. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China