in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya: Babbar jam'iyyar adawa ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka fara tattarawa
2019-02-26 09:49:14 cri

Babbar jam'iyyar adawa a kasar Nijeriya wato PDP, ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi ranar Asabar da ta gabata, wanda hukumar zabe ta kasar wato INEC ta fara tattarawa a birnin Abuja, babban birnin kasar.

Cikin wata sanarwa da shugban Jam'iyyar PDP Uche Secondus ya fitar jiya Litinin 25 ga wata, jam'iyyarsa ta PDP ta ce, ba ta yarda da sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar wato INEC ke bayarwa ba.

Wannan na zuwa ne sa'o'i kalilan, bayan da aka fara tattara sakamakon zaben jiya da rana, inda Shugaban hukumar ta INEC Mahmood Yakubu ke jagorantar zaman karskashin tsauraran matakan tsaro.

Kawo yanzu, ba a karbi 1 bisa ukun sakamakon zaben jihohin kasar 36 ba.

A martanin da ta mayar dangane da ikirarin jam'iyyar adawar, INEC ta ce babu wani dalili na kin amincewa da sakamakon. Tana kuma fatan sanar da wanda ya lashe zaben ba zai wuce ranar Laraba ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China