in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya: An kashe mayakan Boko Haram yayin da suka kai hari kan sasannin sojoji
2019-01-22 09:45:17 cri
Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa, dakarunta sun yi nasarar kashe mayakan Boko Haram da suka kaddamar da hari kan wani sansanin sojoji dake jihar Yobe a yankin arewa maso gabashin kasar, sai dai kuma ba ta bayyana adadin mayakan da aka kashe ba.

Mai magana da yawun sojojin Najeriyar Nureni Alimi ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, sojojin sun shafe sama da sa'o'i biyu suna bata–kashe da mayakan na Boko Haram da yammacin ranar Lahadi, a lokacin da suka kaddamar da hari kan Birget din sojan ko ta kwana ta 27 da kuma makarantar soja ta musamman dake garin Buni Yadi, kimanin kilomita 45 daga garin Damaturu,fadar mulkin jihar Yobe.

Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin sun kuma yi nasarar kwace makamai da albarusai daga hannun mayakan. Amma rundunar ta tabbatar da cewa, sojojinta hudu sun ji kananan raunuka yayin arangamar.

Mayakan na Boko Haram dai sun kaddamar da harin ne, a jiya Litinin sa'o'i 24 gabanin ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari zai kai garin na Damaturu don kaddamar da yakin sake neman zabensa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China