in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya Na Cikin Wani Hali -Sarkin Musulmi
2019-01-31 19:03:10 cri
Kungiyar Jama'atu Nasril Islam dake karkashin jagorancin Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sakwatto, Alhaji Abubakar Sa'ad lll, ta gargadi 'yan siyasar Nijeriya da su guje wa yada kalaman batanci a daidai lokacin da ake dumfarar zaben wannan shekarar. Kungiyar ta kuma bukaci al'ummar Musulmi da su rizimci addu'o'i da fatan Allah Ya sa a yi zabukka lafiya ba tare da wani matsala ba a fadin kasar nan.

Sakataren kungiyar, Dakta Khalid Aliyu, ne ya bayar da sanarwa a madadin Sarkin Musulmin, ya kuma lura da cewa, lallai kasar nan na a ciki wani hali da ake tsanannin bukatar addu'o'i daga dukkan musulmi. Kungiyar ta kuma kara da cewa, "Lallai addu'a na da mahimmanci ga rayuwar musulmi musamman a lokacin da ake fuskantar matsaloli, kamar yadda muke gani a wannan lokacin a kullum garin Allah ya waye, sakamakon harkokin siyasar dake tafe a wannna shekarar 2019, ana kuma sa ran fara zaben ne a watan Fabrairu. "Bukatar rungumar addu'a na da matukar mahimmanci don kuwa babu wani abu da ya fi addu'a a wurin Allah, saboda duk wanda Alllah Ya bude wa kofofin addu'a to lallai Allah zai amsa masa dukka addu'o'insa. "A saboda haka kungiyar Jama'atu Nasril Islam, a karkashin jagorancin Mai Alfarma, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, CFR, mni, ta bukaci amfani da wanna daman na kira ga dukkan al'ummar Musulmin kasar nan da su shiga gabatar da addu'o'i musamman ganin cewa, zaben wannna shekarar na nan, ana kuma gab da farawa. "Wannna kiran ya zama dole ne musamman ganin cewa a matsayinmu na musulmi, addu'a ga Allah shi ne babbar nau'in ibada kuma babu abin da ya Allah Ya fi so daga cikin ibadu kamar addu'a, kuma ta haka ne kawai a ke samun biyan bukata daga gare shi, mu yi fatar samun nasara a zabukkan da za a gudanar na 2019." (Labarin da aka samu daga shafin Intanet na jaridar leadership)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China