in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar zabe a Nijeriya ta dage zaben shugaban kasar zuwa ranar 23 ga wata
2019-02-16 15:21:51 cri

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC, ta sanar da dage zabukan shugaban kasar da na 'yan majalisun tarayya da aka shirya yi yau, zuwa Asabar mai zuwa 23 ga wata.

Shugaban hukumar Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ya gudana yau, kafin fara kada kuri'a.

A cewar Shugaban na INEC, hukumar ta yanke shawarar dage zabukan ne biyo bayan bitar da ta yi cikin tsanaki, kan jigilar kayayyakin zabe da aiwatar da wasu shirye-shiryenta don tabbatar da gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali, inda ta gano cewa gudanar da zabukan a yau ba zai yuwu ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China