Yau Alhamis 28 ga wata, aka bude taro na biyar na zaunannen kwamitin na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ta CPPCC na zama na 13 a birnin Beijing, hedkwatar mulkin kasar Sin.
Taron ya zartas da kuduri kan kiran cikakken zama karo na biyu na kwamitin majalisar CPPCC zama na 13, inda aka yanke sharawar cewa, za a bude taron a ranar 3 ga wata mai zuwa a birnin Beijing. Bisa ajandar taron, za a saurari da kuma tattauna kan rahoton aiki na zaunannen kwamitin majalisar CPPCC da ma shawarwarin da aka gabatar a cikin shekarar da ta gabata. Sa'an nan 'yan majalisar za su halarci taro na biyu na kwamitin babban taron wakilan jama'ar Sin zama na 13 domin sauraro da tattaunawa kan rahoton aiki na gwamnatin kasar Sin da sauran rahotanni, baya ga tattaunawa kan daftarin dokar zuba jari da 'yan kasuwa baki ke yi a Sin. (Kande Gao)