Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce kasar Sin za ta fadada tsarin bude kofa ga sauran sassan duniya, ya na mai jadadda cewa, tsarin na moriyar juna ne.
Da yake jawabi yayin taron manema labarai da aka yi bayan rufe taron majalisar wakilan jama'ar kasar, Li Keqiang ya ce, tattalin arzikin kasar Sin na hade ne da na duniya, ta yadda rufe kofa zai toshewa kasar Sin ta hanyar.
Ya ce, har yanzu kasar Sin ta na da damar fadada bude kofar kasuwanninta, kuma za ta rage kudin harajin kayayyaki da ake shigo da su kasar.
Ya ce, tsarin na bude kofa abu ne da ake yi sannu a hankali kuma mai nisan zango da ya kunshi dukkan bangarori, domin wasu kananan matakan sauye-sauye da aka dauka, za su bada kyawawan sakamako a nan gaba, ya na mai ba da misali da yadda kasuwar yawon bude ido ta kasar ke bunkasa saboda tsarin ba da visa da aka kebe.
Firaministan ya kuma bayyana tsarin bude kofar a matsayin tsari na cude ni in cude ka, ta yadda kowane bangare zai amfana. (Fa'iza Mustapha)