Ga kuma kalaman da shugaban taba ya yi wa al'ummar kasar daga sana'o'i daban daban.
'Yan jarida: Ku mai da al'umma a matsayin malamanku, ku sunkuyar da kai tare da yin natsuwa, ku sa ido a kan hakikanin halin da ake ciki, kuma ku fadi gaskiya, ku gabatar da labarai da ke da tunani da inganci, wadanda za su iya sosa ran al'umma.
Malamai:Ya kamata ku zama jagoran dalibai ta fannin gyara halinsu da samar musu ilmi da koya musu yadda za su yi kirkire-kirkire da kuma bauta wa kasarsu.
Ma'aikatar tsabta birane sun kasance masu gyaran fuskar biranen, wadanda suke gudanar da aiki mai tsarki da martaba. Ni ma mazauni birnin Beijing ne, don haka a madadin mazauna birnin, ina muku godiya.(Lubabatu)