A safiyar yau Talata, aka rufe zagayen farko na taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 a birnin Beijing, inda shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi a karon farko tun bayan da ya sake lashe zaben shugabancin kasar ta Sin.
Cikin jawabinsa, Xi ya jaddada cewa, zai ci gaba da aiwatar da ayyukan da kudin tsarin mulkin kasar Sin ya dora masa, yayin da kiyaye al'ummar kasa cikin himma da kwazo, haka kuma, ya yi amanna cewa, babu wanda zai iya hana ci gaban al'ummar kasar Sin bisa hadin gwiwarmu baki daya. (Maryam Yang)