Zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin ya yi rantsuwar kama aiki da kundin tsarin mulkin kasar
Yau Laraba, zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13, ya gudanar da bikin rantsuwa da kundin tsarin mulki. Shugaban kwamitin Li Zhanshu, shi ne ya shugabanci bikin tare kuma da sa ido a gudanarsa.
A gun taron farko na kwamitin da aka rufe ba da dadewa ba, an nada mataimakin babban sakataren kwamitin, da daraktan sashen kula da aikin kasafin kudi, da darakta na hudu na sashen kula da babbar dokar yankin musamman na Hongkong, da darakta na hudu na sashen kula da babbar dokar yankin musamman na Macau. (Bilkisu)