Mataikin shugaban na Amurka yana wadancan kalamai ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a yammacin jiya Asabar, inda yake zargin cewa, wai kasar Sin na tsoma baki a harkokin cikin gida da ma na zabukan Amurkar, Sannan ya zargi kasar Sin game da manufofinta na cikin gida da na ketare.
Madam Hua ta bayyana cewa, zargin da mataimakin shugaban kasar Amurka ke yiwa kasar Sin ko kadan zancen banza ne da ba su da shaidu, sannan Amurkar ta rude game da abin da yake mai kyau da maras kyau, tana magana ne don kawai duniya ta ji ta. (Ibrahim Yaya)