in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da EU sun shirya taron kare hakkin nakasassu a MDD
2019-02-27 13:07:22 cri

Zaunannun tawagogin kasar Sin da kungiyar Tarayyar Turai a Geneva, sun shirya wani taro kan muhimmancin yarjejeniyar kare hakkin nakasassu cikin hadin gwiwa, da ake wa da lakabi da "kada a manta da wasu" wanda ya gudana jiya a birnin Geneva, inda kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD ke gudanar da taron manyan jami'ai karo na 40.

Yu Jianhua, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD a Geneva da kuma sauran kungiyoyin duniya a kasar Switzerland, ya bayyana cewa, wannan ne karo na farko da Sin da EU suka shirya wani taro cikin hadin gwiwa karkashin inuwar kwamitin kare hakkin dan Adam na MDD, inda ya ce hakan na da ma'ana sosai wajen inganta mu'amala da hadin kai a tsakaninsu ta fuskar kare hakkin dan Adam.

Walter Stevens, zaunennan wakilin EU a Geneva ya ce, EU na son hada kai da Sin wajen inganta mu'amala da hadin gwiwa a fannin harkokin nakasassu da dai sauransu.

Jakadu daga kasashe fiye da 40, da wakilai daga kungiyoyin kasa da kasa da hukumomi masu zaman kansu masu ruwa da tsaki da kwararru masu ilmin kare hakkin dan Adam na Sin da kasashen waje kusan guda dari ne suka halarci taron. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China