Taron da aka yi a wannan karo na tare da dimbin sakamako, wadanda da farko suka shafi ra'ayi daya da Sin da kungiyar EU suka cimma, na yaki da daukar ra'ayin kashin kai, da kuma manufar kariyar ciniki. Inda bangarorin 2 suka yi alkawarin kare tsarin ciniki mai mutunta kungiyar ciniki ta duniya WTO, gami da ka'idojin kasa da kasa, ta yadda za a samu damar kyautata tsarin tattalin arzikin duniya.
Sauran nasarorin da aka samu a wajen taron sun shafi yadda za a hada shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya" ta kasar Sin da tsarin raya tattalin arziki na nahiyar Turai, da hadin gwiwar bangarorin 2 a fannonin tinkarar sauyawar yanayin duniya, da hada-hadar kudi, aikin gona, da dai makamantansu. (Bello Wang)