in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya karrama wasu masana biyu da lambar kimiyya mafi girma
2019-01-08 14:41:49 cri

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya karrama Liu Yongtan da Qian Qihu da lambobin kimiyya mafiya daraja, saboda gudummawar da suka ba da a fagen kimiyya da fasahar kirkire-kirkire.

Xi wanda har ila shi ne babban sakataren JKS kana shugaban askarawar kasar, ya mikawa masanan biyu lambobin yabo da takardun shaida ne, yayin bikin karrama masana, da injiniyoyi da masu bincike da aka saba gudanarwa a ko wace shekara bisa ga nasarorin da suka cimma a wadannan fannoni.

Shi dai Liu Yongtan, malami ne a cibiyar nazarin harkokin kimiyya ta kasar Sin yayin da shi kuma Qian Qihu yana aiki ne a cibiyar nazarin aikin injiniya ta kasar Sin(CAE).

Shugaba Xi ya gaisa da su kana ya taya su murna.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China