in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tauraron dan Adam na Chang'e-4 ya doshi duniyar wata
2018-12-12 19:48:07 cri

Tauraron dan Adam na binciken wata na Chang'e-4 ya doshi duniyar wata a ranar Laraba, matakin da ya zamo muhimmin bangare, na aikin da zai yi, irin sa na farko a tarihi, wato sauka a bangare mafi nisa na duniyar wata.

Hukumar dake lura da harkokin sararin samaniya ta Sin CNSA ta bayyana hakan, tana mai cewa tauraron na hade da na'urar sauka kan duniyar wata da ta bincike, an kuma harba shi ne da rokar Long March-3B. An harba wannan tauraro a ranar Asabar din karshen makon jiya daga tashar Xichang dake lardin Sichuan, a kudu maso yammacin kasar Sin.

Ana sa ran ayyukan da wannan tauraron dan Adam zai gudanar, za su bude wani sabon babi a tarihin binciken duniyar wata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China