A karkashin shirin, daga shekarar 2021 zuwa 2050, kasar Sin za ta kara karfin hukumar ba ma na zama jagora a harkar sufurin jiragen sama ba, har ma na zama cibiyar da za ta yi gogayya a fannin jiragen sama da zirga-zirga, da tsarin hidimar jiragen sama na zamani da na'urorin kula da tashi da saukar jiragen sama na zamani, da matakan tsaro da ingantaccen tsarin gudanarwa.
Bugu da kari, nan da shekarar 2050, kasar tana fatan kara inganta hukumar, ta yadda za ta biya bukatun jama'a, da ma zama jogara a fannin goyayya a duniya, da karfin yin kirkire-kirkire, da gudanarwa. Sauran fannonin sun hada da ci gaba mai dorewa da shiga a dama da ita a harkokin gudanarwar jiragen sama na kasa da kasa.
A shekarar 2017 hukumar zirga-zirgar jiragen saman kasar ta ba da gudummawa sama da kaso 25 cikin 100 na ci gaban zirga-zirgar jiragen sama ta duniya baki daya. (Ibrahim)