in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Amurka suna dab da kammala tattaunawarsu kan tattalin arziki da ciniki
2019-02-25 13:42:33 cri


Kasashen Sin da Amurka, sun samu ci gaba kan wasu batutuwa, biyo bayan tattaunawar baya-bayan nan da manyan jami'ansu suka yi, kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da ta gudana a birnin Washington.

Yayin tattaunawar da ta gudana daga ranar 21 zuwa jiya 24 ga wata, wadda kuma ita ce zagaye na 7 da suka yi, tun bayan fara irin tattaunawar a watan Fabrairun bara, jami'an kasar Sin da Amurka sun aiwatar da wasu muhimman matsaya da shugabannin kasashensu suka cimma, yayin ganawar da suka yi cikin watan Disamba a kasar Argentina, inda suka mayar da akalar tattaunawar tasu kan daftarin yarjejeniya.

Wakilan kasar Sin sun ce an samu ci gaba a bangarorin da suka hada da musayar fasahohi da kare hakkin mallakar fasaha da sana'ar ba da hidima da harkokin gona da shingayen cinikayya da ba na haraji ba da farashin musayar kudade. Sa'an nan shugaba Donald Trump na Amurka ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa, zai jinkirta amfani da karin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasarsa da aka shirya fara amfani da shi a ranar 1 ga watan Maris.

Kasashen Sin da Amurka sun samu sabon ci gaba na daban wajen warware rikicin da ke tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya. Kasashen 2 sun samu ci gaba na a-zo-a-gani a maimakon cimma ra'ayi daya kawai, sun kuma fara tattaunawa kan abubuwan da za a tanada cikin yarjejeniya. Sun kara mai da hankali kan kananan abubuwa, masu ruwa da tsaki na dab da cimma yarjejeniya.

Ma iya cewa, kokarin da Sin da Amurka suke yi na kara samun moriyar bai daya ya taimaka wajen samun ci gaban a-zo-a-gani a yayin tattaunawarsu, inda bangarorin 2 suka samu sakamako ta fuskar daidaiton ciniki da batun tsare-tsare.

Dangane da daidaiton ciniki, kasar Sin za ta kara sayen amfanin gona, kayayyakin makamashi, da hidimomi daga Amurka, wanda zai sassauta kulawar da Amurka ke nunawa kan rarar kudi da kasar Sin ta samu a fannin sayar da kayayyaki zuwa Amurka, haka kuma zai taimaka wajen biyan bukatan jama'ar Sin na jin dadin rayuwa, da kara azama kan kyautatuwar tsarin masana'antun kasar Sin.

Dangane da batun tsare-tsaren tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Amurka, Amurka ta gabatar da wasu bukatu, wadanda suka shafi moriyar kasar Sin, akidar tunani, da tsaron kasa. A sa'i daya kuma, wasu bukatun da ta gabatar sun dace da yadda kasar Sin take kokarin zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga kasashen waje, da neman samun bunkasuwar tattalin arziki yadda ya kamata. Alal misali, kare ikon mallakar ilmi ya zama tilas ga duk wata kasa dake kokarin raya kanta ta hanyar kirkire-kirkire, haka kuma a kan tanadi shi cikin tsarin cinikayya na kasa da kasa. A matsayinsu na manyan kasashen tattalin arziki guda 2 da ke kan gaba a duniya, kuma manyan kasashen da suke kan gaba a duniya ta fuskar kirkire-kirkire da cinikayya, kasashen Sin da Amurka sun gabatar da bukatun bai daya da kuma samun moriyar bai daya wajen kare ikon mallakar ilmi. A shekarun baya da suka wuce, sau da yawa aka tanadi kare ikon mallakar ilmi cikin takardun sakamakon da aka samu yayin tattaunawar kasashen 2. A yayin tattaunawar da aka gudanar a wannan karo, kasashen 2 sun sami ci gaba na a-zo-a-gani kan batun na kare ikon mallakar ilmi, wanda ya nuna bukatun bai daya na kasashen 2 da kuma moriyarsu ta bai daya.

Tattaunawar da ke tsakanin Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya ta yi kama da wani aiki mai wuya. Sun kara yin taka tsan-tsan yayin da suke dab da kammala tattaunawar. Ko da yake batun tattalin arziki da ciniki da Sin da Amurka suke daidaitawa yana da wuya kuma yana da sarkakiyya, amma ba su da lokaci mai tsawo na tattaunawa, domin kwanaki 90 kawai suke da shi, kuma akwai jan aiki a gabansu. Yanzu tawagogin kasashen 2 sun fara tattaunawa kan abubuwan da za a tanada cikin yarjejeniya bayan sun rubanya kokarinsu ba dare ba rana, sun shiga lokaci mafi wuya kuma mafi muhimmanci. A kokarin kiyaye moriyar kasashensu 2, tabbas tawagogin za su yi tunani sosai da sosai kan abubuwan da za a tanada cikin yarjejeniyar. Amurka ta sanar da jinkirta amfani da karin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasar, wanda aka shirya fara amfani da shi a ranar 1 ga watan Maris. Hakan ya bai wa bangarorin 2 karin lokaci domin samun moriyar bai daya, da kara kokarin cimma yarjejeniyar samun moriyar juna da nasara.

Kasar Sin za ta ci gaba da nuna sahihanci da kara yin kokari wajen yin tattaunawar, tare da fatan Amurka ita ma za ta dauki matakai masu ruwa da tsaki, a kokarin kara samun moriyar bai daya. Haka zalika kuma kasar Sin za ta gudanar da ayyukanta kamar yadda ta tsara, za ta tinkari sauye-sauyen da aka samu a duniya bisa sanin ya kamata, karkashin manufar zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China