Daga bangare na daban, babban sakataren MDD António Guterres, da yawancin wakilai masu halartar taron sun jaddada cewa, za su kiyaye ra'ayin bangarori daban daban da daukar matakai tare. An fara yin takara a tsakanin masu kiyaye ra'ayin bangarori daban daban da masu kiyaye ra'ayin bangare daya, da kuma a tsakanin masu kiyaye ka'idojin duniya da masu raina ka'idoji a dandalin MDD a halin yanzu.
Taken babban taron MDD a wannan karo shi ne "mai da MDD ta zamo mai tasiri ga dukkan mutanen duniya, da raya zamantakewar al'umma mai zaman lafiya da adalci, da dorewa, ta hanyar raya karfin bada jagoranci da rarraba aiki a duniya". Ana fatan shugabanni da wakilai masu halartar taron za su bada ra'ayoyi game da wannan batu. Amma shugaba Trump ya sake kin amincewa da bin wannan tunani.
Kamar yadda ya bayyana a gun babban taron MDD karon da ya gabata, shugaba Trump ya yi bayani game da manufar maida moriyar kasar Amurka a matsayin gaban komai da ya aiwatar bayan da ya zama shugaban kasar Amurka, kana ya zargi hukumar hakkin dan Adam ta MDD da kotun manyan laifuffuka ta duniya, da sauran hukumomin bangarori daban daban da yarjejeniyar batun nukiliya na kasar Iran, kana ya zargi kasashen Iran da Venezuela da Jamus, tare da gabatar da tunanin yaki da ra'ayin bangarori daban daban na kasar Amurka. Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Amurka suka bayar, an ce, jawabin shugaba Trump ya maida wakilan kasa da kasa masu halartar taron su yi zargi, da kin amincewa da ra'ayinsa.
Alal misali, babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya nuna cewa, a lokacin da muke fuskantar babban kalubale, ya kamata mu hada kai wajen warware matsalar bisa halin da muke ciki. Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya kuma yi kira ga kasa da kasa, da su ki "ka'idar bin mai karfi". Kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU ta kuma sanar da cewa, za ta ci gaba da yin cinikayya da kasar Iran, da kuma kafa sabon tsarin biyan kudade, domin magance takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa kasar. Haka kuma, shugaban kasar Afirka ta Kudu Matamela Ramaphosa, ya yi kira ga kasashen duniya da su hada kai wajen yaki da duk wanda yake son bata tsarin ciniki a tsakanin kasa da kasa, da kuma duk wanda yake son hana dunkulewar kasa da kasa. Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kuma bayyana cewa, ya kamata mu kiyaye ikon MDD cikin harkokin kasa da kasa, domin shimfida yanayin zaman karko a nan duniya.
Kasar Amurka ita ce daya daga cikin masu kafa tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa bayan yakin duniya na biyu, amma, bayan shekaru sama da 70, gwamnatin kasar Amurka ta wannan karo ta fara aiwatar da manufar son kai, bi da bi, ta janye jikinta daga yarjejeniyar abokantaka ta na yankunan kewaye tekun Pacific wato TPP, da yarjejeniyar sauyin yanayi na Paris, da kuma yarjejeniyar nukiliyar Iran, haka kuma ta janye jikinta daga hukumar kyautata ilmi, kimiyya da al'ada ta MDD wato UNESCO, da kuma kwamitin kare hakkin dan Adam, da wasu hukumomin kasa da kasa, ta kuma tashe takaddamar ciniki ta hanyar kara harajin kwastan a duk fadin duniya. Lamarin da ya kasance babbar matsala da ta kawo wa tsarin ciniki dake tsakanin kasa da kasa, wanda ya hana ci gaban zamantakewar al'umma. Tabbas ne dukkanin kasashen duniya za su nuna kiyayya kan harkokin da ta yi. (Zainab, Maryam)