180927-maryam.m4a
|
Kwanan baya, gwamnatin kasar Sin ta fidda takarda "Game da takarddamar cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, da matsayin kasar Sin kan wannan batu", inda ta yi bayani kan dangantakar cinikayya dake tsakanin kasar Sin da kasar Amurka. Cikin takardar, an jaddada cewa, bai kamata a maida harkokin ciniki cikin 'yanci a tsakanin kamfanonin kasar Sin da na kasar Amurka ciniki na tilastawa kamfanonin Amurka da su mika fasahohi ga kamfanonin kasar Sin ba, saboda babban ci gaba da kamfanonin kasar Sin suka samu a fannin raya fasahohi, wannan zargin da Amurkar ta yi ba gaskiya ba ne, kuma ya saba da yarjejeniyoyin da aka kulla.
Dangane da wannan batu, ga karin bayani da Maryam Yang ta hada mana:
Alal hakika, tun bayan da kasar Sin ta fara bude kofa ga waje, ya zuwa yanzu shekaru 40 da suka shude, a cikin wadannan shekaru 40, kamfanonin kasashen ketare sun kafa huldar abokantaka da kamfanonin kasar Sin, da kuma kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kamfanonin Sin, bisa aniyarsu ta habaka sabbin kasuwanninsu a kasar Sin, da rage kudaden da suka kashe wajen yin kire-kire, da kuma tsawaita lokacin yin amfani da tsoffin fasahohinsu, lamarin da ya kasance harkokin ciniki na ganin dama ke nan.
Mataimakin shugaban kwalejin nazarin fasahohin sadarwa na kasar Sin Wang Peng ya bayyana cewa, zargin da kasar Amurka ta yiwa kasar Sin cewar Sin ta tilastawa kamfanonin Amurka da su mika fasahohinsu ga kamfanonin Sin, ba shi da tushe. Ya ce, "Da farko, A cikin dokoki, ciki har da takardu da manufofin da gwamnatin kasar Sin ta fitar, babu sharudan da suke tilastawa kamfanonin ketare da su mika fasahohinsu ga kamfanonin kasar Sin. Na biyu, mai yiyuwa ne akwai musayar fasahohi a tsakanin kamfanin hadin gwiwar Sin da kasashen ketare, amma wannan ya kasance shawarwarin kasuwanci dake tsakanin kamfanonin biyu, gwamnatin kasar Sin ba ta sanya hannu cikin batun ba, kuma ba wanda ya tilastawa wani da ya mika fasahohinsa. Na uku, kamfanonin kasar Sin sun sami wasu fasahohi bisa dimbin kudaden da suka kashe, a maimakon tilastawa kamfanonin ketare da su mika fasahohi gare su."
Haka kuma, Wang Peng yana ganin cewa, zargin da kasar Amurka ta yiwa kasar Sin shi ne wata hujjar da ta rike domin ta da takaddamar cinikayya a tsakaninta da kasar Sin.
"Burin kasar Amurka shi ne ta da takarddamar ciniki dake tsakaninta da kasar Sin, ta yadda za ta hana bunkasuwar tattalin arziki da sana'o'in fasahohin zamani na kasar Sin. Wannan shi ne ainihin dalilin da ya sa kasar Amurka ta fidda wannan zargi kan kasar ta Sin."
A hakika dai, mika fasahohin da aka yi tsakanin kamfanonin kasashe masu ci gaba da na kasar Sin ya faru ne bisa tunanin kamfanonin kasashe masu ci gaba wajen samun babbar moriya, da kuma ayyukansu na kaurar da masana'antunsu zuwa kasar Sin. Tun daga shekarun 1990s, ya zuwa yanzu, kamfanonin kasar Amurka da suka hada da Microsoft, Intel, Procter & Gamble wato P&G a takaice da dai sauransu sun ci gaba da kafa cibiyoyin nazari a kasar Sin, domin habaka kasuwanninsu a nan kasar Sin.
Wang Peng ya ce, cikin shekaru da dama da suka gabata, kamfanonin kasar Amurka sun cimma moriya matuka bisa mika fasahohin da suka yi da kamfanonin kasar Sin, sune mafi samun moriyar hadin gwiwar fasahohi.
Haka kuma, a lokacin da yake tsokaci kan wannan batu, mataimakin ministan harkokin kasuwancin kasar Sin Wang Shouwen ya bayyana cewa, cikin dokokin kasar Sin, takardu da manufofin gwamnatin Sin, ba a taba tilastawa kamfanonin ketare da su mika fasahohinsu ga kamfanonin kasar Sin ba. Ya ce, "Idan wani kamfanin ketare yana son zuwa kasar Sin domin zuba jari, a mafi yawan lokuta, yana iya kafa kamfani mai jarin bangare daya kadai, kuma babu batun mika fasahohi ga irin wannan kamfani. A sa'i daya kuma, idan wani kamfanin ketare yana son zuwa kasar Sin domin kafa wani kamfanin hadin gwiwa, to wannan kamfanin ketare da kamfanin hadin gwiwarsa na kasar Sin su biyun za su yi shawarwari na hadin gwiwa, domin kulla yarjejeniya a tsakaninsu cikin yanayi na adalci. Lamarin da ya kasance zabin da kamfanonin suka yi da kansu cikin 'yanci, bisa shawarwarin da suka yi cikin yanayin adalci, amma gwamnatin kasar Sin ba za ta tsoma baki cikin lamarin ba, kuma ba za ta tilastawa wani ba." (Maryam)