in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Donald Trump na kara zubar da amanarsa a yunkurinsa na cutar mutane
2018-08-03 14:27:26 cri





A ranar 1 ga wata, wakilin harkokin cinikayya na kasar Amurka Robert Lighthizer ya sanar da cewa, shugaba Trump ya umurce shi da fara tunani kan kara sanya kudin haraji kan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurka din wadanda darajarsu ta kai dala biliyan 200, wato daga kaso 10% zuwa 25%, a wani yunkuri na sa kaimin kasar Sin ta sauya kudurinta.

Abin lura shi ne, a yayin da fadar White House ke ikirarin kara kudin haraji da take sanyawa, tana kuma ta watsa labaran neman farfado da shawarwari tare da kasar Sin. A game da wannan, ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta yi nuni da cewa, yadda kasar Amurka ta yi fatali da moriyar kasashen duniya, har ma ba ta kula da moriyar manoma da 'yan kasuwa da kuma masu sayayya nata, tana ta matsa wa kasar Sin lamba amma kuma tana neman yin shawarwari da ita, matakin ba zai haifar da kowane tasiri ga kasar Sin ba, kuma a maimakon haka, zai sa kasashe da shiyyoyi da ke kyamar yakin cinikayya faduwar gaba.

A ja-in-ja da Sin da Amurka suka yi a harkar cinikayya cikin tsawon watanni hudu da suka wuce, kasar Amurka ta yi ta rasa amanarta a matakan da ta dauka. Daga dala biliyan 50 zuwa biliyan 200, domin neman zabe ne shugaba Trump ya yi ta daukar matakan kara sanya kudin haraji, sai dai bai yi zaton halin ko-in-kula da kasar Sin ta nuna ba, don haka ba yadda zai yi sai ya yi barazanar kara sanya kudin haraji a kan gaba dayan kayayyakin da kasar Sin ke fitarwa zuwa gare ta. Amma Amurka din ta wuce gona da iri, ba ta kai ga cimma burinta ba, har ma ta jawo kyama da raini daga al'ummar duniya.

In an yi la'akari da halin da ake ciki a duniya, Amurka tana da karfin da kusan wanda ya fi na kowace kasa ta fannonin siyasa, da tattalin arziki, da aikin soja da kuma kimiyya. To, shin me ya sa take ta daukar munanan matakai na cutar sauran kasashe, har ma da kawayenta. In mun yi nazari, hakan na da alaka da yanayin siyasa da fadar White House ke ciki yanzu.

Na farko, shugaba Trump ya taba zama wani dan kasuwa mai nasara sosai. A yayin da yake takarar neman shugabancin kasar Amurka, ya lashi takobin "sake daukaka kasar Amurka", har ma ya shiga fadar White House tare da wasu akidun kasuwanci, kuma ya cusa abin da yake kira "fasahar ciniki" a huldar da ke tsakanin kasa da kasa. Duk da haka, mulkin kasa ya sha banban da kasuwanci, yadda yake gudanar da harkokin kasarsa da ka'idojin kasuwanci, mataki ne na rashin sauke nauyin da ke bisa wuyansa, haka kuma ya zubar da martabar kasarsa.

Na biyu kuma, a sama da shekara guda da ta wuce, masu tsattsauran ra'ayi da suka hada da wakilin harkokin cinikayya na kasar Amurka Robert Lighthizer, da ma darektan kwamitin kula da harkokin cinikayya na fadar White House Peter Navarro sun samu rinjaye. A labarin da jaridar New York Times ta bayar, an ce, su wadannan mashawarta masu tsattsauran ra'ayi ne da suka ba da shawarar sanya kudin harajin da ya kai kaso 25% a kan kayayyakin da darajarsu ta kai dala biliyan 200 da kasar Sin ke fitarwa zuwa Amurka. A ganinsu, matakai na kara wahalar kasar Sin su ne hanya mafi kyau a burin dawo da kasar Sin teburin shawarwari. Ban da haka, kwanan nan ma shugaba Trump ya sake dawowa da tsohon babban mashawarcin fadar White House, Steve Bannon, wanda a watan Agustan bara ya bata da shugaban, don ya ba da shawarwari kan batun kara daukar kwararan matakai na sanya haraji.

Tun bayan da ta tada yakin ciniki a kan kasar Sin daga ranar 6 ga watan da ya wuce, ko kadan gwamnatin Trump ba ta cimma wata nasara ba, lamarin da ya hana Amurka din ta hura wutar yaki zuwa sauran sassan duniya, don haka kuma take damuwa. A ja-in-ja da ta yi da kasar Sin cikin watanni hudun da suka wuce, mai yiwuwa ne Amurka ta gane cewa, kasar Sin ta samu goyon baya daga sassa daban daban, amma gwamnatin Trump na kara fuskantar matsin lamba daga sassan gida da waje, a sakamakon yadda ta yi gaban kanta, ta tada yakin ciniki tare da lalata moriyar al'ummar kasar ta. Amma kuma ta rasa abin da za ta yi, don haka ta yi ta yin barazana. Sai dai kasar Sin ba ta tsoron barazana, kuma al'adar al'ummar Sinawa ne su kara mutunta wadanda suke mutunta su. Idan Amurka din ta yi ta yin barazana tare da lalata moriyar kasar Sin da ta al'ummarta, ba shakka kasar Sin za ta mayar da martani, don kare kanta. Matsayin kasar Sin ne a daidaita sabani ta hanyar yin shawarwari, amma da sharadi, wato zaman daidaito tare da rikon amana. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China